Muhimman abubuwa shida da suka faru a zaɓen shugaban ƙasar Amurka

Muhimman abubuwa shida da suka faru a zaɓen shugaban ƙasar AmurkaA daidai lokacin da ake dakon sanar da Donald Trump a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka, ga wasu muhimman abubuwa guda shida da suka faru.


Donald Trump ya samu nasarar yin kome a fadar shugaban ƙasar bayan doke Kamala Haris.

Zuwa yanzu Trump ya samu nasarar wuce ƙuri'u wakilan zaɓe guda 270 da ake buƙata domin zama shugaban ƙasa - tun da farko, a jawabinsa da magoya bayansa a Florida ya ce ya samu gagarumar nasara.

Trump ya yi kamfe ne da alƙawarin inganta tattalin arzikin ƙasar - inda ya yi alƙawarin yaƙi da hauhawar farashi - da tsuke iyakokin ƙasar domin hana kwararowar baƙin haure da gina katangar tsakanin Amurka da Mexico.

Har yanzu ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen daga wasu jihohi, ciki har da masu muhimmanci guda uku - Nevada da Michigan da Arizona.

Wani sauyi da aka samu shi ne yadda jami'iyyar Republican ta ƙwace rinjayen majalisar dattawa.

Har yanzu Kamala Haris ba ta ce komai ba, duk da magoya bayanta sun taru domin ji daga gare a Washington DC, kafin suka watse.

Post a Comment

0 Comments