Daga Mohammad A. Isah.
Gwamnatin jihar Katsina a karo na biyu, ta sake kaddamar da jami'an tsaron al'umma wato "Katsina State Community C-Watch" a turance.
Taron kaddamarwar da yaye a lokaci guda, ya gudana ne a ranar Juma'ar nan a Kwalejin Jami'an Tsaron Farin kaya na Civil Defence da ke Katsina.
A yayin da yake jawabi a wajen yaye jami'an, gwamna Radda, ya bayyana yadda gwamnatinsa da al'ummar jihar ke ganin nasarar wadancan jami'an tsaron al'umma da aka yaye irin wadannan a shekarar bara, tayadda suke samun nasarori a wajen yaki da 'yan'tadda da suka addabi wasu yankunan jihar.
Gwamna Radda ya jajanta da nuna alhini bisa wasu jami'an tsaron suka riga mu gidan gaskiya a yayin artabu da 'yan ta'adda a mabambantan lokuta, sannan ya yi kira ga al'ummar jihar da su bada gudummuwar wajen ba wa wadannan jami'ai hadin kai don ganin jihar ta samu zaman lafiya mai dorewa.
"Zaman lafiyar jihar katsina ba zaman lafiyar gwamna ba ce, zaman lafiyar al'ummar jihar katsina ne baki daya ce. Don haka, hakki ne a gare mu mu tashi tsaye mun taimaka masu domin mu samu tsaron da ya kamata mu samu a jihar Katsina." Ya yi kira.
Taron kaddamar da sabbin jami'an da aka yaye, ya samu halartar Kwamishin 'yansandan jihar da sauran daukacin jami'an tsaro a jiha har ma da na wasu makwaftan jihohi.
Daga cikin wadanda suka yi jawabi da karafafa wa jami'an gwiwa a taron akwai: Kwamishin 'yansandan jihar CP Aliyu Abubakar Musa, Kwamishinan tsaron cikin gida, Dr. Nasiru Mu'azu Danmusa, da Mataimakin shugaban Kwalejin Civil Depence na Jihar, Babangida Abubakar Dutsin-ma.
Sabbin Jami'an da aka kaddamar su kimanin 550 wadanda suka fito daga kananan hukumomin jihar guda goma, tuni a wajen taron gwamnan ya hannanta masu Motoci, Babura da Bindigogi da sauran makamai don tsare dukiyoyi da rayuwar al'umma yankunansu, tare da yi masu addu'o'in nasara.
0 Comments