Daga Moh'd A. Isa.
Gwamnatin jihar Katsina a ranar Juma'ar nan, ta kaddamar da kwamitin da ta kafa na mafi karancin Albashi na Naira 70,000 ga ma'aikatan jihar Katsina.
Da yake kaddamar da kwamitin, mataimakin gwamnatin jihar Katsina, Honorabul Faruk Lawal ya bayyana kwamitin a matsayin wanda zai duba tare da bada shawarwari na mafi karancin albashin ga ma'aikatan fadin jihar da kananan hukumominta.
Jobe, ya bayyana takaicinsa na yadda hauhauwar farashin kayan masarufi a fadin kasar nan wanda janye Tallafin Manfetur ya haifar, inda ya bayyana mafi karancin albashin na Naira 70,000 abin da ya mafi dace daga gwamnatin Kasar zuwa ga ma'aikata, wanda jihar Katsina ita ma ta bi sahu aiwatar da hakan kamar sauran jihohi:
"Wannan kwamiti an ba shi alhakin ya kawo wa gwamnati shawarwari na yadda za a aiwatar da wannan tsari na mafi karancin albashi na Naira 70,000, sannan an ba kwamitin Sati 3 ya gabatar da rahotansa ga gwamnati domin aiwatarwa."
Membobin kwamitin da gwamnatin ta ba wa alhakin duba mafi karancin albashin sun hada da: Sakataren gwamnati, Abdullahi Garba faskari, Shugaban ma'aikata na jiha, Kwamisshinan kasafin Kudi da tsare-tsare, Kwamishinan Kudi, Kwamishinan kanan hukumomi da harkokin cikin gida, Babban Ma'ajin gwamnatin jiha, Shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jiha, Shugaban bangaren bincike ba jiha, Shugaban bincike na kanan hukumomi, Shugaban Kungiyar kwadago ta jiha, Wakilin NELGO, Shugaban ALGON, da babban sakataren 'Yan Fanso.
Honorabul Faruk ya kuma hori kwamitin da ya gudanar da aikinsa cikin lokacin da aka dibar masa domin gwamnati ta aiwatar cikin hanzari.
Daga karshe Honrabul Jobe, ya yi wa Kwamitin fatan samun nasarar aiwatar da wannan aiki da aka ba shi.
0 Comments