Rahotanni daga Magamar-jibiyar jihar Katsina na shigo wa Zamani media cewar, wasu 'yan bindiga sun yi dirar mikiya a garin a daren jiya Talata.
Rahotannin sun ce, 'yanta'addan sun kwashi mutane sun tafi da su cikin Daji. Sannan a yayin kwasar mutanen, sun dauke hankalin mutane ta hanyar banka wa gidan wani Mutum mai suna Aliyu Yahaya dan yaro wuta, inda gidan ya ci ya cinye kurmus, ba a fitar da ko tsinke ba.
Yankin Jibiya dai na daga cikin wuraren da 'yan bindiga suka addaba a jihar ta katsina, tayadda da wuyan gaske a yi kwanki biyu zuwa uku ba tare da sun yi ta'adin Dukiya ko salwantar da Rai a yankin ba.
0 Comments