Anya Kama Mamallakin Sahar Telegram Paval Durov Ba Siyasar Gwamnatocin Kasashen Turai Ba Ce?

Wasu rahotanni daga kasar Faransa na bayyana cewar, hukumomin tsaro a kasar Faransa suna rike da shugaban Telegram, Pavel Durov. 

Rahotannin sun ce an kama shi ne da yammacin ranar Asabar din nan bayan da jirginsa (Private Jet) ya sauka a wani filin saukar jirage a gefen birnin Paris na kasar Faransa.

Rahotannin sun ci gaba da cewar, jami'an tsaron sun rike Pavel Durov da sunan suna zarginsa da kin bayar da bayanai cikakku a kan wasu kungiyoyin 'yanta'adda da suke amfani da sahar Telegram tare da 6oye kudaden Sata da kudaden Safarar miyagun kwayoyi da ake yi a kan dasahar "TON Blockchain" wadanda suka ce mallakin Pavel Durov ne, kuma yana da masaniya a kan masu yin hakan.

Sai dai har ya zuwa yanzu babu wani tabbataccen bayani a hukumance game da kama Pavel Durov din ko wani sharhi ko karin haske daga gwamnatin kasar Faransa din.

Masu sharhi na ganin cewar, muddin ta tabbata Faransa ta kama Pavel Durov, to hakan na nuni da tsokanar kasar Rasha da magana ko neman rikici. Domin kuwa, Pavel Durov dan kasar Rasha ne, ita kuma Rasha ba ta ga-Maciji da Faransa.

A yanzu haka wasu hukumomi a kasar Rasha sun ce sun bayar da Awanni ga kasar ta Faransa na ta saki Pavel Durov ko kuma su san abin da za su dauka na mataki.

Har wayau masu sharhi na bayyana cewar, batun kama Pavel Durov Siyasa ce da kuma neman samun wasu bayanan sirri game da kasar Rasha da wasu manyan mutane da ke s kasar Rasha. Faransa ta yi haka ne domin ta tilasta Pavel Durov bayyana musu bayanan da suke son samu a kan Rasha da wasu sirrorinta.

Masu tsokaci kan kamun, sun ci gaba da cewar babban abin da zai nuna siyasa ce shi ne yadda manyan kafafen watsa labaran kasashen Turai suka yi shiru akan kamun kamar su BBC, CNN, VOA, MBC da sauransu.

Duk a fikin zantukan mauu sharhin, sun ci gaba da bayyana cewar, a wani 6angaren kuma zai iya yiwuwa Elon Musk ake hari, domin Elon Musk da Pavel Durov su ne mutanen da a yanzu suke da kafar sadarwar da suke gudanuwa ba irin yadda gwamnatocin Turai ke so ba.

A yanzu duniya ta watsar da kafofin sadarwa da kasashen Turai suke da ikon juya su, irin BBC, VOA, CNN, France 24 da sauransu, an koma kan X Twitter da Telegram, wanda hakan ya sa ake samun 'yancin fadin albarkancin baki wanda gwamnatocin turai ba su ji dadi ba.

Post a Comment

0 Comments