Daga Wakilinmu Tare Da Muhammad Kwairi Waziri.
An gano wani Jirgin Kwale-kwale wanda ya yi kusan Shekaru 100 da 6acewa karamar hukumar Dukku da ke jihar Gombe.
Bayan binciken shekarun kwale-kwalen dogaro da wasu abubuwa da aka gani a jikinsa, an kiyasta cewar kwale-kwalen zai iya kai shekaru 100 ko ma ya wuce haka.
Bayanai sun ce ruwan Kogi ne ya tono jirgin kwale-kwale wanda ake sa ran ya 6ata ne tun a shekarun baya a cikin Kogin Hashidu, inda yanzu haka an fito da Kwale-kwalen daga cikin ruwa, ganin yadda mutane suke ziyartarsa a garin.
Kamar yadda kamwannin kwale-kwalen suka bayyana, Jirgi ne wanda aka sassake shi sassaka irin ta mutanen da, kuma yanzu haka jirgin zai iya ci gaba da aiki domin ingancin kirarsa, sai dan abin da ba a rasa ba na 'yan gyare-gyare duba da canjin Zamani.
0 Comments