Labari daga Jihar Katsina na shigo kana cewar, tuni Jami'an tsaron farin kaya, DSS sun kama matashin da ya jagoranci zanga-zangar tsadar rayuwa danake fama danita a Nijeriya, a Jihar Katsina.
Kamar yadda Katsina Reporters ta ruwaito, Matashin wanda dan gwagwarmaya ne, kuma sakataren gamayyar kungiyoyin fararen hula na jihar Katsina, wato Kwamared Kabir Shehu Yandaki an kama shi ne bayan da ya jagoranci zanga-zangar lumanar tsadar rayuwa a jihar Katsina a ranar Alhamis.
Matashin Comrade Kabir Shehu Yandaki dai, na daga cikin matansan da suka jagoranci zanga-zangar yunwa da aka fara gudanarwa a fadin Nijeriya, wanda jihar Katsina ke daya daga cikinsu.
0 Comments