Rundunar 'Yansanda ta jihar Kano, ta kama Hasan Ilya wanda ake zargin kasurgumin shugaban gungun 'yan fashi ne masu cin karensu babu babbaka a jihohin Katsina da Kano, Zamani Media ta ruwaito.
Kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yansanda na Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana wa Manema labadu a ranar Talatar nan, ya bayyana yadda suka kama Hasan Ilya a tsakiyar dare a karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano, yana kokarin tsallakewa cikin daji a kan babur din sa.
Ya ce kama shi na zuwa ne bayan da suka samu korafin wani Magidanci daga karamar hukumar Kunci ta jihar Kano, cewar wasu mutane sun shiga gidansa sun yi masa fashin Naira Miliyan 15, inda daga nan suka bazama nemansu, inda a karshe suka kama wanda ake zargin cewar shugabansu ne, mai suna Hasan Ilya.
A yayin da suka yi tara-tarar kama wanda ake zargin, SP Kiyawa ya ce sun same shi da Bindigogi AK47 guda 2 a cikin Buhu, Harsasai guda 47 da muma tsabar kudi har Naira Miliyan 4,986
Tuni dai an mika shi a sashen bincike na manyan laifuka da ke Bompai dominnkara tattara bayanai kamin daga bisani a iza keyarsa zuwa Kotu, kamar yadda Jami'in rundunar 'yansadar ya bayyanar.
Duk da matsalar tsaron da ake fama da ita musamman a jihar Katsina, hakazalika kuma ana fama da fashi da makami a wasu yankuna na jihar da makwabtanta, wanda haka ke kara ta'azzara matsalar tsaro da fatara a tsakanin al'umma.
0 Comments