Rahotanni daga Jihar Kano na shigo mana cewar, wata gobara da har yanzu ba a tantance ce musabbabin afkuwar ta ba ta shi a masarautar Kano, inda ta babbake babbar fada da karagar mulki ta sarkin Kano da ke a Kofar Kudu.
Binciken 'Yansanda ya bayyana cewar gobarar ta faru ne da misalin karfe 11 na daren jiya Juma'a.
Rundunar 'yansandan Kano sun bayyana cewar, an gano yadda aka lalata mukullin shiga fadar na baya, amma ana ci gaba da bincike, kamar rahotan yadda Northern Broadcasters ta ruwaito.
0 Comments