‘Yan majalisar dokokin jihar Rivers dake goyan bayan tsohon gwamnan jihar, Wike, sun dakatar da duk wani kashe-kashen kudi da Gwamna Fubara zai yi har sai ya sake gabatar da kasafin kudi a gaban majalisar.
A makon da ya gabata ne dai ‘yan majalisar suka bada wa’adin kwanaki 7 ga Gwamnan na ya sake gabatar da kasafin kudin inda wa’adin ke cika a yau.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Major Jack ne ya gabatar da kudurin hana gwamna kashe kudaden.
Bayan amincewa da kudurin majalisar ta yanke shawarar rufe asusun tattara haraji na jihar tare da dakatar da gwamnan daga yin amfani da kudaden jihar
0 Comments