Afeni Shakur Davis mahaifiyar 2 Pac (asalin sunanta shi ne Alice Faye Williams. An haife ta ne a ranar 10 ga Janairun 1947, ta mutu a ranar 2 ga watan Mayu 2016.
Ita din 'yar gwagwarmayar Siyasar Amurka ce, kuma memba a Kungiyar Black Panther Party. Ta kafa gidauniyar 'Tupac Amaru Shakur Foundation', kuma ta yi aiki a matsayin Shugaba na Amaru Entertainment Inc. kamfanin rikodin da shirya fina-finai.
An kama Afeni Shakur tare da wasu 'yan Kungiyar Neman Hakkin Bakaken Fata ta 'Black Panthers' guda 20 wanda aka fi sani da Panther 21 a wani farmakin da 'Yansanda suka kai kafin wayewar gari a ranar 2 ga Afrilun 1969. Daga karshe dai an wanke 'yan Kungiyar Panther 21 daga tuhumar da ake yi musu a shekarar 1971, amma ban da Afeni, domin ita ta ci gaba da kasancewa a gidan Yari tana dauke da juna biyun Tupac. Tana a kurkukun ne ta haifi 2 Pac.
Wannan wata wasiƙar da Afeni din ce ta rubuta daga gidan Yar wadda Jaridar Panther ta buga a ranar 7 ga Watan Yunin 1969.
-Saliaddeen Sicey
0 Comments