Daga Mohammad A. Isa.
Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Honorabul Farouq Lawal Jo6e zai zama gwamnan jihar Katsina na tsawon wata guda cur daga ranar Alhamis mai zuwa.
Kasancewarsa gwamnan jihar, zai faru ne a dalilin amincewar da Majalissar dokokin jihar ta yi ne na bukatar da gwamnan jihar, Dr. Dikko Umar Radda ya gabatar wa majalissar na tafiya hutun wata daya.
Gwamna Radda ya mika bukatar amincewar Majalissar, inda ya bayyana mata cewar yana son ya tafi hutu wanda ya shirya tafiya daga ranar Alhamis 18 ga watan Yulin 2024, zuwa 18 na watan Agustan 2024.
A cikin wasikar da gwamnan ya aike wa majalissar, ya nemi ta amince da mataimakinsa, Honorabul Alhaji Farouq Lawal a matsayin wanda zai rike jihar har zuwa lokacin karewar hutun da ya dauka.
Tuni dai Majalissar ta amince da bukatar gwamnan bayan da ta karanta wasikar a zamanta na yau Talata, 16 ga Yuli, 2024.
0 Comments