Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya yaba gami da jinjinawa hukumar kula da jin dadin alhazzai ta kasa bisa jajircewar da ta yi wajen samun gudanar da aikin hajjin Bana.
A hannu guda gwamnan ya yabi Gwamnatin tarayya bisa kyakkyawan tsari da ta samar wanda ya kai ga nasarar aikin hajjin bana, wanda a fili yake an cimma wannan nasarar ne sakamakon haÉ—in gwiwa tsakanin gwamnatin da ta hukumar Alhazzan.
Yabon na Gwamnan na zuwa ne biyo bayan sauyin shugabancin hukumar da aka samu karkashin jagorancin Alhaji Jalal Arabi, wanda shugabancin nashi ya kawo kyakkyawan cigaba a hukumar.
Bayanai sun bayyana aikin hajjin bana na shekarar 2024 ya samu gagarumar nasara duk da manyan kalubale da aka fuskanta, wanda hakan ya sanya Æ™warin gwiwa ga jama’a kan Gwamnatin tarayya.
“A yayin da Æ™asa Najeriya ke cikin matsalolin na matsin tattalin arziki, amma Hukumar zabe ta samu nasarar aiwatar da aikin hajji lallai babu shakka wannan abin a yaba ba”.
0 Comments