Daga Wakilinmu.
A yau Asabar ne, 'yan'uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Alzakzaky na sassan kasar nan suka yi tururuwa zuwa Kano, a inda suka cika filin taro na Filin gidan Sarki, Mazansu da Matansu
Wakilin Zamani Media ya labarto mana cewad, Makasudin taron dai domin yi wa wasu yaransu walimar Saukar Al-kur'ani mai tsarki, inda suka haddace shi tsab.
Da ma dai duk shekara, mabiya mazhabar ta Shi'a na gudanar da irin wannan taro a Kano na taya yaran nasu murna bisa ga haddace Al-kur'ani mai girma, inda yaran daga sassan kasar nan ke haduwa waje guda a yi masu wannan kasaitaccen taron, sai kuma wata shekara a yi wa wasu da suka sake haddacewa daga baya.
Wakilin Zamani Media ya ce, an yi tsammanin bayyanar Shehin Malami, Sheikh Alzakzaky a taron domin gabatar da jawabi, amma saboda wasu uzururrukan bai samu halarta taron ba, a maimakon haka ya gabatar da jawabin ne ta hanyar Majigi, a yayin jama'a ke ji ganinsa a Majigin.
Da ma dai kafin nan, Shehunnan Malamai daga cikin almajiran Malamai sun gabatar da jawabai a taron.
0 Comments