Wasu rahotanni daga jihar Kano na shigo mana cewar, an fara samun wasu 'yan siyasa na kawo wa al'ummar maza6arsu da abubuwa binne Gawa.
Ratanni sun bayyana haka din ne a dalilin kawo irin wadannan kayayyaki na binne gawar ne da wani Sanata a Kano ya yi ga al'ummar maza6arsa.
Sanatan Kano ta tsakiya, Rufa'i Hanga ne ya badanirin wadannan kayayyaki a matsayin tallafi ga alummar birnin kano, inda ya gwangwaje su da kayayyakin rufe gawa da suka hada da Makarar daukar Gawa, Likkafani da kuma Tukwanen Binne Mamata a Kabari.
Abin tambaya dai a nan shi ne ne, shin al'ummarsa ne suka bukaci hakan a matsayin abin da suka fi bukata a cikin daukacin ayyukan da maza6ar tasa ke bukata, ko kuwa gatse ne ya yi masu na halin matsayin rayuwar da ake ciki wato su je su karasa shi babu ruwansa?
0 Comments