Sojojin Nijar Sun Kama Kasurgumin Danbindigar Da Ya Addabi Njeriya Da Nijar.


Sojojin Jamhuriyyar Nijar da ke aikin sintiri a jihar Maradi wadanda ake yi wa lakabi da "Farautar Bishiya", sun yi nasarar damke wani kasurgumin dan ta'addan wanda ya addabi wasu garuruwan da ke iyakar jam'huriyyar Nijar da Nijeriya.

An kama kasurgimin dan ta'addan, Adamu Ɓaleru, tare da wasu 'yan ta'adda 65, a yayin da suke yunkurin kai wasu hare-hare a kauyukan Nijeriya.

Kamar yadda hukumomin Sojin kasar suka bayyana a ranar Laraba, sun ce sun kama 'yan ta'addan ne a wani Kauye mai suna "Kowa Gwani", a yayin da suke tsaka da shiryen-shiryen kai hari zuwa wasu garuruwan da ke kasar Nijeriya, Zamani Media ta ruwaito.

Post a Comment

0 Comments