Shugaba Ra'esi Na Iran Ya Rasu.

Rahotanni daga Kasar Iran na bayyana cewar, jirgin nan mai saukar Ungulu na shugaban kasar da ya yi 6atan dabo sakamakon gur6atar yanayi da ruwa mai karfi a ranar Lahadi, an gano cewar ya yi hatsari.

Hukumomi sun tabbatar cewar shugaban Iran, Ebrahim Ra'esi, ministan harkokin wajen ƙasar, da sauran wasu 'yan rakiyarsu mutane 6 sun rasu a wani hatsarin jirgin nasu da auku a yanki da ke kusa da kan iyaka da Azerbaijan na kasar.

In dai ba a manta ba, a ranar Lahadi Zamani Media ta kawo maku Labari 6atan dabon jirgin sakamakon gurbatar yanayi da ruwa mai karfi da aka samu a Kasar, inda muka bayyana cewar har ma an same su cikin lafiya, sai dai wannan labarin ya shafe wancan labarin duba da labarin rasuwarsu da hukumomin kasar suka bayyanar.

Masu aikin ceto dai sun 6ata tsawon Yini da daren ranar Lahadin suna neman jirgin, wanda daga karshe aka gano cewar ya samu hatsari.

Post a Comment

0 Comments