Daga Wakilinmu.
Kamfanin nan na'urorin Microsoft, yana duba yiwuwar barin Nijeriya a cikin watan Julin nan mai zuwa, Zamani Media ta ruwaito.
Kamfanin na shirin yin haka ne saboda wasu matsalolin da suka taso wadanda suke ganin ba za su iya ci gaba da aiki a Kasar ba.
Kodayake ba su kai ga bayyana matsalalin da za su kai su ga barin kasar ba tukunnan, amma masharhanta na ganin tabbas bai rasa nasaba kare-karen haraji da gwamnatin kasar ke yi wa Kamfanoni, rushewar Tattalin arziki da hauhauwar farashin kayayyaki da ci gab da yi a Kasar, wanda hakan ke ci gaba da durkusar da kanana har ma da manyan masana'antu na ciki da wajen kasar da aaiki a kasar.
Kamfanin Microsoft dai suna Ofishoshi guda biyu: daya a jihar Lagos din Nijeriya, daya kuma jihar Nairobin kasar Kenya. Ofishinsu da ke Nijeriya shi ne suka bayyana shirin rufe shi a watan Yuli mai zuwa.
Idan aka rufe Kamfanin na Nijeriya, hakan zai kara kawo rashin ayyukan yi ga kasar, domin sama da mutune 560 ne za su rasa ayyukan yi a Kamfanin muddin rufe Kamfanin ya tabbata a watan Julin.
Zamani Media ta labarto cewar, masu sharhi ne bayyana cewar matukar Kamanin na Microsoft ya bar Nijeriya, to hakan zai haifar da babban gi6i da kuma ci baya mai muni a kasar, kuma da wahala wani Kamfani irinsa wannan ya zo Nijeriya a nan kusa don aiwatar da irin ayyukansa duba da yadda tattalin arzikin kasar yake tangal-tangal.
Microsoft dai ya fara aiki ne a shrkarar 2022 a kasar, wato ya shafe shekaru biyu kenan inda daruruwan 'yan kasar suke aiki a cikinsa.
0 Comments