Rahotanni daga kasar Iran na shigowa Zamani Media cewar, jirrgin sama mai saukar ungulu wanda ke ɗauke da shugaba kasar Iran a ranar Lahadi, Ra'isi ya samu tangarɗa a sama saboda guɓatar yanayin da ake fama da shi a Kasar, wanda ya sa dole jirgin ya yi saukar gaggawa.
Lamarin dai ya faru ne a yanki Jolfa da ke Arewa maso gabashin ƙasar ta Iran, inda tawagar ceton gaggawa na jami'an kasar suka yi gaggawar kai dauk inda lamarin ya afku.
Ya zuwa yanzu dai, rahotanni sun tabbatar da cewar duk wanda ke a cikin jirgin babu wanda ya sami rauni ko makamancin haka, suna sauka cikin kaoshin lafiya.
0 Comments