Shugaban kamfanin, Richard Teng ne ya bayyana haka a wani shafin intanet, kamar yadda jaridar New York Times ta wallafa.
A cewar rahoton na jaridar ta New York Times, Tigran Gambaryan, jami'i a a kamfanin, ya yi iƙirarin cewa ya samu wani saƙo mai ɗaga hankali a wata tafiya da ya yi zuwa Najeriya a watan Janairu.
Rahoton ya ce "a wata ziyara zuwa Najeriya a watan Janairu, Tigran Gambaryan, jami'i a kamfanin Binance mai hada-hadar kirifto, ya samu wani saƙo mai tayar da hankali. An bai wa kamfanin kwana huɗu su biya dala miliyan 150 a kuɗin kirifto,"
Gambaryan, wanda tsohon jami'in tsaro ne a Amurka, ya fahimci saƙon a matsayin neman na goro daga wani a gwamnatin Najeriya, a cewar wasu mutum biyar da suka san da batun da kuma nazarin saƙon da jaridar New York Times ta yi.
Shi da abokan aikinsa na Binance sun gana da Æ´an majalisar dokokin Najeriya da suka zargi kamfanin da kauce wa biyan haraji da kuma barazanar kama ma'aikatan kamfanin."
Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne kafin a kama Gambaryan da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla bisa umarnin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro, Nuhu Ribadu.
Daga bisani kuma Anjarwalla ya tsere inda aka gano shi a Kenya.
A martaninsa, kakakin ofishin Ribadu, Zakari Mijinyawa ya bai wa gwamnati tabbacin bin ƙa'ida.
0 Comments