Daga Wakilinmu.
Rahotanni sun bayyana wa Zamani Media Crew cewar, tsohon dan takarar jami'iyyar PDP a za6ukan shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi wata ganawar sirri ta musamman da wasu kusoshin jam'iyyar a ranar Larabar nan a jihar Katsina, inda suka tattauna wasu muhimman batutuwa da suka ji6inci jam'iyyar.
Kamar yadda Zamani Media ta samu rahoton ganawar, ganawar ta kunshi wakilcin wasu jama'a ne daga masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da suka hada da Tsohon dan takara Gwamna a Jam'iyar PDP wato Honorabul Ahmed Aminu Yar'adua, Tsohon Sanata na Shiryar Katsina wato.. Sanata Umar Ibrahim Tsauri, Ciyaman na yakin neman za6en 2023 kuma tsohon Sakataren Jam'iyar PDP matakin Kasa, tsohon Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Dr. Mustapha Muhammad Inuwa, tsohon dan takarar gwamna a Jam'iyar PDP kuma mataimakin Daraktan kula da harkokin zabe na 3023, Shehu Inuwa Imam, da Alhaji Mustapha Musa Yar'adua.
Kodayake ba a bayyanawa Zamani Media yadda ganawar ta gudana da kuma a kan me aka yi shi ba, amma ta samu labarin cewar an yi ganawar ne bisa wakilcin sauran masu kudirin ciyar da Jam'iyar gaba, da ku?a yi mata fatan nasara a za6e mai zuwa idan mai duka Allah ya kai mu.
0 Comments