Daga Wakilinmu.
Rahotanni daga jihar Kaduna na shigo wa Zamani Media cewar, wasu Jama'a gari sun hana turbude wasu Gawarwaki guda hudu a Makabartar hayin Rigasa a ranar Asabar din nan.
Kamar yadda rahotanni suka bayyanar, sun ce tun da farko wasu mutane ne wadanda ba a san ko suwaye ba, suka sauke Gawarwaki guda hudu daga cikin Motar Asibiti wato Ambulance, inda suka kutsa kai da su cikin Maƙabartar Layin Bola da ke Unguwar Rigasa, da nufin rufe su.
Rahoton ya ci gaba da cewar, sai dai Mutanen ba su nemi izinin hukumar kula da Makabartar ba, wanda hakan ya sa jama'ar yankin ba su gamsu ba, bayan da suka sami labari, sai suka yo tururuwa zuwa makabartar, suka yo waje da gawarwakin domin a cewarsu ba su san gawarwakin na su wane ne ba, da kuma dalilin Mutuwarsu balle a zo a rufe su a Makabartarsu.
Sai dai iuma, shaidun gani da ido sun bayyana cewar, jama'ar sun dauki doka a hannunsu, tayadda a maimaikon su hannata ko su kai rahoton lamarin ga hukuma, sai kawai suka banka wa Motar wuta, mutanen cikinta kuma suka shige cikin mutane gari suka sulale abinsu.
Ya zuwa hada wannan Rahoto dai, hukumomi ba su ce uffan ba kan lamarin, ita kuma mota na a wajen da aka kone ta.
0 Comments