In Da Gwammati Za Ta Mayar Da Ko Da Da Tallafi Dala Kaya Za Su Sauko Da Kashi 60% A Nijeriya, -Dangote

Shararren attajirin ɗan kasuwar Afrika a Nijeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewar 'yan Nijeriya sun kafa masa ƙahon zuƙa suna son dole sai sun zuƙe masa jini.

Ɗangote ya ce mafi yawan jama'a suna ganin tamkar yana da hannu a tsadar rayuwar da ake fama da ita a halin yanzu a ƙasar musamman tsadar kayan masarufi.

"Kai bari in gaya muku gaskiya, wannan tsadar rayuwar daga Allah take, shi kaÉ—ai ne ke iya yaye mana ita. Amma akwai laifin gwamnatin tarayya." In ji shi.

Ya ci gaba da cewar " Ni kaina na fi Æ´an Nijeriya shan wahalar wannan tsadar rayuwar, saboda dukkan kayan da nake fitar wa tun daga Sugar, Fulawa, Siminti, Gishiri, Maggi, dukkansu da Naira nake siyar wa 'yan Nijeriya su, ni kuma da Dollar nake zuwa in shigo da kayan haÉ—insu." In ji shi

Ya kara da cewar, "Dalar Amurkar nan kuma kowa ya san farashinta a halin yanzu. Ko mutum bai je makaranta ba, ya san farashin dala a wannan lokaci, Ni kaina na rasa Market Control. Idan na siyar wa dilolina, kaya suka biya ni da naira, idan na canja ta zuwa dala sai in ga na yi mummunar faÉ—uwa. Domin kuwa kuÉ—in ba sa isa ta in sake siyo kayan haÉ—in da na yi a baya, balle a yi maganar riba." Ya koka

Ya ce, " Saboda haka, don Allah kada kowa ya zarg e ni! Wannan matsalar duk gwamnatin tarayya ce ta haddasa ta sakamakon janye hannunta daga ba wa naira kariya. Ta cire tallafin dala da kuma na man fetur duk a lokaci É—aya." Ya bayyanar.

Dangote ya kuma yi kira da cewar, "Ina kira ga ƴan Nijeriya tun da dai su suka fito suka zaɓi gwamnatin nan, to su tabbatar ta yi musu abin da suke so."

"Ko da ba a mayar da tallafin mai ba, to su roƙe ta da ta mayar da tallafin Dala. Ina tabbatar musu ko shi kaɗai aka mayar, duk farashin kayan nan zai rikito da kashi 60% cikin 100 da gaggawa, idan kuma ba haka ba, nan da zuwan watan biyar lokacin da gwamnatin nan za ta cika shekara ɗaya da rantsarwa muna hasashen buhun Sugar a kamfani ma sai ya kai mana naira dubu 150."

Post a Comment

0 Comments