Daga Mohammad A. Isah.
Sunan Allah(T) mai dauke da kalmar "Allahu" da rubutun Larabci ya bayyana a jikin wani Dankalin Hausa (Sweat Potato) a Katsina.
Lamarin dai ya faru ne a Unguwar Sabuwar Kofa Katsina a lokacin da wata mai tuyar Dankali da Awara mai Suna Firdausi Sani ke cikin Tuya a ranar Talatar nan da ta gabata.
A lokacin da wakilinmu Muhammad A. Isah ke zantawa da ita dangane da lamarin, Firdausi Sani ta bayyana masa cewar, ita dai yadda abin ya faru shi ne wani yaro ne ya zo ya ce ta ba shi Dankali amma mai zafi yake da bukata, inda ta debo dankalin ta zuba shi a cikin Mai don ta toya masa...
"Ina zuba Dankalin, sai take-yanke Wutar ta Mutu. Tana mutuwa, sai na ga Man shi ma ya yi sanyi baki daya." In ji ta.
"Na sa itatuwa na fita na fita, amma wutar ta ki ta kama."
Nana Firadusi ta ce, dayake a lokacin duhu ya fara, sai ta aika aka dauko mata wayarta a cikin gida inda ta haska don ta ga me ke faruwa...
"Ina haskawa, na motsa Dankalin haka, sai na ga sunan Allah a jikin wannan Dankali. Amma jikinsa bai soyu ba." Ta nuna shi.
Ta ci gaba da cewar, abin mamaki "Na aje shi (dankalin) a gefe guda, ina kunna wutar; sai ta kama ta ci gaba da soya min Dankali."
Dangane da Matakin da ta dauka a kan Dankalin mai dauke da suna Allah a yanzu, ta ce yanzu ta dauki shawarar wasu mutane ne da suka ce a bar shi ya bushe a haka, sai a daka shi a rika sha idan bukatar hakan ta taso ga marar lafiya.
Sunan Allah da na Manzonsa(S) da kuma Ayoyinsa dai sun sha bayyana a jikin abubuwa daban-daban kama a jikin Itatuwa, Ganyayyaki har ma da jikin Dabbobi da Mutane. Sannan kuma, an sha ganin wasu halittu irinsu Kwari kamar; Gizo-gizo, Gara, Tururuwa, Rina lo Kudan zuma da sauransu ke saka ko zana sunan Allah, na Manzonsa da sauran sunayen Allah a jikin Sakarsu.
Ko me samun Ayoyin Allah ko na Manzonsa a jikin irin wadannan abubuwa ke alamtawa?
0 Comments