Halittu: Yadda Nau'in Tsuntsun Cuckoo Yake


Akwai wani nau'in tsuntsu mai suna CUCKOO (common cuckoo). Yanayin kalar gashinsa yana shige da na shaho (hawk)

Macen wannan tsuntsu tana da wata É—abi’a da ake kira da PARASITIC BROODING, wata hanya ce da wasu halittun masu saka kwai ke bi don kaucewa wahalhalun kyankyasa da raino.

Idan macen Cuckoo za ta yi ƙwai ta kan nemi sheƙar wasu ƙananun tsuntsayen masu yin ƙwai mai shigen kala da nata ta faki idon mai sheƙar ta kwatsa nata ƙwan ba tare da mai sheƙar ta ankare ba. Sai dai girmansa na iya bambantashi da sauran.

Wani abun mamaki, a yayin saka kwan tsuntsunwar na da dabarar rage adadin kwayayen da ta tarar a shekar kafin ta saka nata don ragewa danta wahalar gasa (competition) da kuma gudun mai sheqar ta gane an yi mata kari.

Idan azal ta hau mai sheƙar ba ta gane an mata kwatse ba, sai ta haɗa ta rungume har baƙon ƙwan da tunanin shi ma nata ne. Ita za ta yi kwancinsu ta ƙyanƙyashe. Matsalar na farawa ne daga zarar wannan baƙon ƙwan ya ƙyanƙyasu.

Idan baƙon ne ya fara ƙyanƙyasuwa, abu na farko da ɗan zai fara shi ne tabbatar da yin juyin mulki a sheƙar ta hanyar tunkuɗo ƙwayayen mai sheƙar na asali ƙasa ɗaya bayan ɗaya da bayansa tare da taimakon fuka-fukansa. Ba zai samu nutsuwa ba har sai ya tabbatar shi kaɗai ya rage a sheƙar.

Idan kuma tare-tare suka Æ™yanÆ™yasu da Æ™wayayen mai sheÆ™ar, to nan ma babu makawa zai yi wa sobawan zamansa juyin mulki ne ta hanyar saÉ“a su a bayansa yana cicciÉ“o su É—aya bayan É—aya yana jefo su waje daga sheÆ™ar har sai ya ji saura shi kaÉ—ai a sheÆ™ar. Ko da sun riga shi Æ™yanÆ™yasuwa kuwa da zarar ya Æ™yanÆ™yasu to su ma abin da zai aikata musu kenan duk da sun fi shi kwanaki kasantuwar yana da girman jiki da saurin girma kwarai fiye da su. 

Uwar da ya kashewa É—iya ita za ta yi ta dawainiyar renonsa (ciyarwa), shayarwa da ba shi kariya a tsammanin nata ne har ya girma ya kama gabansa.

Bugu da kari tsuntsuwar ba ƙwai ɗaya take ba... sai dai tana hikimar rarraba ƙwayayenta a sheƙar tsuntsaye daban-daban ne maimakon ta juyewa tsuntsuwa daya a shekarta don kar tsuntsuwar ta gane. Misali in ta yi guda a wannan shekar tsuntsuwar sai ta je ta wata tsuntsuwar ta yi wani.

Ita Æ™wanta yana da saurin Æ™yanÆ™yasuwane saboda tana da  fara kwancin Æ™wan tun yana cikinta har sai ya fara nuna take fid da shi wata tsuntsuwar ta Æ™arasa mata Æ™yanÆ™yasar.

Wato a takaice nau'ikan wannan tsuntsayen da ke da wannan dabi'a uwar da ta saka kwansu ba ita ke kyankyasa da renon su ba. Sai dai ta kai kwan wata sheƙar a renar mata su. Saboda dabi'arsu ta kin gasa (competition) sukan jefo diya da kwayayen mai shekar kasa su gaje sheƙar da uwar.

Aliyu Umar M. Gumel.

Post a Comment

0 Comments