Daga Mohammad A. Isah.
Makarantar Firamare ta "Jabiru Abdullahi Memorial Primary School Katsina", ta gudanar da taron hutun karshen zango karatu na farko, zangon da ya kare a ranar Juma'ar nan, 12 ga Disamba 2023.
A yayin gudanar da taron hutun, daliban Makarantar sun gudanar da abubuwan ban sha'awa, birgewa gami da jan hankali, wanda hakan ya saka Sakatariyar ilimi a matakin farko ta Jihar Katsina (Ministry Of Basic And Secondary Education) kuka riris.
Abubuwan da yaran suka gabatar a taron sun hada da: wakokin al'adun Hausa da wakokin kiranyen kan a daina yi wa mata auren wuri, wanda "Hasua/Fulani Club" suka gabatar.
Sauran abubuwan su ne: Gabatar da Tarihin Makarantar, shugaban Makarantar da kuma tarihin Sakatariyar hukumar Ilimi ta yanzu Dr. Halima Umar Kofar Sauri, wanda "Press Club" suka gabatar: sai kuma Fareti na musamman.
Da take jawabi a matsayinta na bakuwa ta musamman a taron, Sakatariyar Hukumar Ilimin, Dr. Hajiya Halima Umar, ta bayyana jin dadinta kan yadda yaran suka gudanar da wadancan abubuwa masu faranta rai.
Dr. Halima Umar ta kuma yaba wa malaman makarantar bisa ga jajircewarsu da irin salon koyarwarsu ga daliban.
Ta ce, a lokacin da ta ga yaran na taka Faretin, ba ta san sadda ta fashe da kukan farin ciki ba, inda ta bayyana cewar ba ta tunanin akwai wata Makarantar Primary ta gwamnati a fadin jihar da ta kai wannan Makaranta, da ma dai makarantar ta yi shura da cirar Tuta kan kwazon dalibanta a cikin sauran makarantun gwamnatin jihar.
Haka zakali, ES Hajiya Halima Umar, ta bayyana irin aniya da shirin da gwamnatin jihar karkashin shugabancin Malam Dikko Umar Radda take da shi wajen bunkasa harkokin Ilimi a fadin jihar.
Shi ma a nashi jawabin, shugaban Makarantar, Malam Jabir Kabir ya gode wa gwamnatin jihar kan yadda take ba wa harkar ilimi muhimmanci a jihar, tare da ba wa makarantarsa kulawa, inda ya bukaci gwamnatin Dr. Dikko Radda ta dore da hakan.
Wadanda suka halarci taron Hutun sun hada da: Dr. Hajiya Halima Umar, da Jami'i na musamman a hukumar Ilimi a matakin farko, Alhaji Muntari Isah, masu kula da makarantun firamare a shiyyoyi (E.Os) shugaban kungiyar Malamai da Iyayen Yara(PTA), da kuma Iyayen Yara da sauran baki.
Abin da ke biye, kundin hotunan taron Hutun ne.
0 Comments