Daga Mohammad A. Isah.
Ana zargin wata mata mai suna Hafsat da Mijinta Alhaji Dayyabu da kashe wani Matashi mai suna Alhaji Nafi'u a jihar Kano.
Lamarin dai ya faru a karamar hukumar Tarauni da ke jihar Kano a ranar Larabar nan.
Mamacin Matashin mai suna Alhaji Nafi'u mai shekaru shekaru 36, shi aboki ne kuma ubangidan Alhaji Dayyabu, wanda ake zarginsa shi da matarsa Hafsa da kashe Matashin, Alhaji Nafi'u.
A yayin wata fira da manema labarai, da mahaifin Mamamacin a ranar Laraba, Malam Hafizu Salihu Gorondo, ya bayyana wa manema labarai cewar, abokin dan nasa Alhaji Dayyabu ya 6oye masa kisan da suka yi wa dan nasa da farko, a lokacin da ya kira shi yake sanar da shi cewar dansa Alhaji Nafi'u ya rasu.
Ya ce, da ma dan nasa na kwance a Asibiti yana jinya bisa ga wani aiki da aka yi masa, inda abokin nasa da matarsa suka yi amfani da wannan damar suka kashe masa da.
Mahaifin ya ci gaba da cewar, sun gane cewar kashe shi aka yi a lokacin da suka zo suka tarar da har an yi masa wanka an shirya shi, ana shirin yi masa jana'iza, inda a lokacin da suka bude gawar tasa domin bankwana, sai suka ga alamun an caccaka masa wasu abubuwa a wuya, lamarin da ya tada masu hankali suka san lallai mutuwar tasa akwai lauje cikin nadi, kuma ba su yi wata-wata ba suka sanar da 'yansanda.
Mahaifin ya kara da cewar, wanda ake zargin, Alhaji Dayyabu ya kira wani Malami wanda ya taya Dayyabu kimtsa Nafi'u bayan an kashe shi, inda ya ce shi ma suna zarginsa da 6oye Hujja.
Ya kara da cewar, a lokacin tuhumar Matar Alhaji Dayyabu, a gaban su ta amsa wa jami'an tsaro cewar ita ta taya Mijin nata kashe Matashin, inda ta cacca masa wuka a wuya.
Da yake amsar tambayar da aka yi masa na matakin da zai dauka a matsayinsa na mahaifin mamacin, Malam Hafizu cikin shasshekar kuka, ya ce suna kira da hukuma da ta yi masu adalci wajen binciken, don a hukunta wadanda suka kashe masa dansa Nafi'u wanda ya fi so a duk duniyar nan sakamakon kyautata masanda yake yi.
Tuni dai hukumar 'yan sanda ta shiga cikin lamarin inda take gudanar da bincike, inda ake saurarensu sakamakon binciken nasu, kodayake har ya zuwa hada wannan rahoton ba su ce uffan ba tukunna.
Hotunan da ke kasa, wadanda ake zargin ne Alhaji Dayyibu da Matarsa Hafsat rike da dansu, a yain da dayan hoton kuma mamacin Alhaji Nafi'u Hafiz ne.
0 Comments