Daga Mohammad A. Isah.
An gudanar ta taron gangamin zagayowar ranar cutar nan mai karya garkuwar jiki Kanjamau/Sida wadda aka fi sani da HIV/ AIDS a turance a Katsina.
Kamar sauran garuruwa, hukumar yaki da cutar mai reshe a jihar katsina, KATSACA, ta bi sahun takwarorinta na wasu jihohin Nijeriya wajen gudanar da gangamin a ranar Alhamis din nan.
A yayin gudanar da gangamin, hukumar tare da wasu kungiyoyi sun zagaya manyan Titunan birnin na katsina, inda suka rika Wakoki tare da daga kwalaye da Alluna masu dauke da rubutun "Yaki da cutar HIV/AIDS", tare da kuma wayar da kan jama'a kan a daina kyamatar masu cutar.
Duk a cikin gangamin, hukumar tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi sun fadakar tare da tunatar da masu dauke da cutar cewar su kasance masu bin tsarin shan magungun da aka dora su a kai, don tsawaitar garkuwar jikinsu ba tare da cutar ta lahanta su ba.
Shugaban hukumar yaki da cutar na Jihar Katsina, Dr. Bala Nuhu Kankia ne ya jagoranci gangamin.
A jawabin da ya gabatar a wajen gangamin, shugaban hukumar ya yi kira da al'ummar a kan cewar masu dauke da cutar Sida/Kanjamau din nan fa na bukatar tallafin al'umma.
"Suna bukatar mu janyo su cikinmu su zama abin kauna gare mu." In ji shi.
Ya ci gaba da cewar, "mu kula su kulawa ta musamman domin su ma al'umma ne." Ya jaddada.
"Mu koya masu mahimmancin shan magani, domin zai taimaka masu wajen gudanar da al'amurransu na yau da kullum." Ya karfafar
Majalissar dinkin duniya dai ta ware ranar 30 ga Nuwambar kowace shekara, don tunawa tare masu cutar da kuma yaki da cutar Kanjamau a duniya.
0 Comments