Wata babbar kotun jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga kan Sarkin Fulanin jihar Kwara, Alhaji Usman Adamu, da dan'uwansa, da wani Gidado Idris, bisa samunsu da laifin hada baki na yin garkuwa da wani bawan Allah.
An yanke wa mutanen uku hukuncin daurin rai da rai a ranar Alhamis.
An zarge su da yin garkuwa da Abubakar Ahmad, kuma ana zarginsu da kar6ar kudin fansa har Naira miliyan daya kafin a sake shi bayan shafe kwanaki 20 a hannunsu.
Lamarin satar mutumin ya faru ne a tsakiyar shekarar 2022.
Daraktan shigar da kara na jihar Kwara (DPP), Idowu Ayoola, ya gabatar da wadanda ake tuhuma uku a gaban kotu bisa zargin hada baki wajen yin garkuwa da wani mutum.
A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Adenike Akinpelu, ta ce mutanen uku duk sun amince da aikata laifi, inda ta ce ko a jikinsu ba su yi da nasanin abin da suka aikata ba.
Ta ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun kama wanda ya shigar da kara suna masu ikirarin cewa shi mai garkuwa da mutane ne domin kar6ar kudi daga gare shi.
0 Comments