Daga Mohammad A. Isah.
Bayan kammala taron zikirin Juma'a na shekara-shekara na Kasa tare da gudanar da addu'ar samun zaman lafiya a Nijeriya, a Katsina a ranar Juma'ar nan 3 ga nuwamban 2023, Shaikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya samu wakilcin babban dansa, Sayyadi Ibrahim Dahiru Usman Bauchi ya ziyarci Manyan Malamai a jihar ta Katsina.
Malaman da shehin ya ziyarta manya-manya sun hada da Shaikh Yakubu Musa Hasan daga 6angaren kungiyar Izala, sai kuma na 6angaren 'yan'uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Yaqoub Alzakzaky, wato Shaikh Yakubu Yahaya Katsina.
Sayyidi Ibrahim Dahiru Bauchi da tawagarsa sun ziyarci Malaman ne a wani mataki na sada zumunci da samun hadin kai a tsakanin al'ummar Musulmi, da kuma fatan samun zaman lafiya mai dorewa musamman ga abubuwan da ke faruwa na ta6ar6arewar tsaro a yankin Arewa maso Yamma da kasar baki daya.
A yayin ziyarar, Shehunan sun gana da junansu, inda suka tattauna musamman dangane da abin da ya shafi al'ummar Musulmi a kasar nan tamu da ba mu da kamarta, tare da fatan samu haduwar kanuwa a tsakanin al'ummar Musulmi.
A ziyarorin biyu da Sayyadin ya yi, an kuma aiwatar da addu'i na musamman ga al'ummar falasdinu da fatan samun nasararsu ga haramtacciyar kasar Isra'ila da ta mamaye su tsawon shekaru yanzu take yi masu mummunan kisa ga yara da mata da tsofaffi... daga karshe aka yi hotunan tarihi aka yi Sallama.
A ta 6angaren Shehin Malami, Shaikh Yakubu Yahaya ya gabatar wata kyauta wa Sayyadin zuwa ga babban shehi, Shehu Dahiru Usman Bauchi.
0 Comments