Kotun Musulunci Ta Umarchi Coci Ta Rantsar Da Kirista Da Littafin Bible A Kano.

Daga Ado Danladi.

Babbar Kotun Shari'ar Musulunci da ke kofar Kudu karkashin mai shari'a Ibrahim Sarki Yola, jihar Kano, ya ummarci wata Coci da ta rantsar da wani Kirista ai suna Yakubu Tumoti da littafin baibul domin kauce wa zargin da wani matashi ya yi masa cewa sun ba shi ajiyar mashin mai kafa 2 lifan an sace.

Tun da farko dai matashin mai suna Mahmud Yusuf Kofar Nasarawa, ya shigar da kara kotu ta kwato masa Mashin din sa da ya je Magaji Rumfa domin yin Booking na filin Bal da za su yi.

Ya ce a nan suka tambayi Tumoti inda za su ajiye mashin din nasu kuma a nan take ya nuna musu, sai dai bayan ajiyewar sun dawo dauka amma sai suka tarar babu nasu a wajen. 

Ya ci gaba da cewar, ko da suka tambaye shi sai ya ce ya ga wasu wai sun tura sun yi gaba da shi.

Ko da mai Shari Ibrahim Sarki Yola ya numfasa ya mai da tambaya ga wanda ake zargi, Tumoti, sai ya ce shi sam atafau ba su ba shi wani ajiyar mashin ba; hasali ma shi bai taba ganin su ba, tun da shi aikinsa a wajen ya bude Gate a shigo ko a fita ne.

Tuni mai Shari'a ya tambayi Tumoti cewar, a matsayinsa na Kirista ko ya yarda a yi masa Shari'a a nan Kotun ta Musulunci, ko a kai su kotun Magistrate. Kuma nan take Yakubu Tumoti ya ya roki da a yi masa Shari'ar a nan, wanda hakan ya sa Sarki Yola ya umarci sifeto Sulaiman daya daga cikin ma'aikatan kotu da Rajistara da su je da Tumoti Cocin da yake gabatar da Ibadarsa da babban malaminsa ya rantsar da shi kan cewa ba shi ne ya dauki Babur din ba, kuma ba isan wanda ya dauka ba, kuma ba a hada kai da shi an dauka ba, kuma hasali ma bai san su ba.

Mai Shari Ibrahim Sarki Yola ya dage ci gaba da shari'ar zuwa ranar 4 ga watan Disamban wannan shekara ta 2023.

Post a Comment

0 Comments