Daga Mohammad A. Isah
Birnin Katsinan Dikko, ya sake samun kawatuwa da sabon katafaren gidan Mai a ranar Larabar nan.
Shahararren Kamfanin rukunin gidan man nan na "Danmarna Petroleum Nigeria Limited" ne ya kaddamar da sabon gidan Man, don kara wa al'ummar jihar samun saukin wajen nemowa da amfani da Manfetur a birnin.
Taron kaddamar da gidan Man wanda ya gudana a farfajiyar sabon gidan Man da aka bude wanda ke daura da Shataletale Kofar 'Yandaka a birnin katsina, an aiwatar da shi ne a ranar Laraba, 8 ga Nuwanban 2023.
Da yake jawabi a yayin kaddamar da gidan Man, shugaban Kamfanin rukukin gidajen Man na "Danmarna Petroleum Nigeria Limited", Alhaji Dahiru Usman Sarki, ya yi wa Allah godiya bisa ga wannan ni'ima da ya yi masa wadda har ta sa ya sake bude wani sabon gidan Mai don saukawa al'ummar birnin jerangiyar samun Manfetur.
Usman Sarki ya kuma hori musamman ma'aikatansa da su ci gaba da kasancewa masu yin aiki bisa gaskiya da kuma rikon Amana tare da tarairayar kwastomomi, da ma dai don su ake yin wannan Kasuwa, domin ko ba komai "Mutane su ne Kasuwa..."
Taron kaddamar da sabon gidan Man ya samu halartar ma yan mutane, 'yan kasuwa, Jami'an tsaro da kuma 'Yanjarida.
Daga cikin wadanda suka halarci kaddamarwar akwai shugaban rukunin Kamfanin Manfetur na "AA Rahamawa" Alhaji Aminu Wali, da Shugaban Kamfanin rukunin gidajen Manfetur na "Dakare Nigeria Limited" Alhaji Lolo Dakare, da sauran manyan baki.
0 Comments