An Shirya Wa Masu Amfani Da Shafukan Sada Zumunta Taron Kara Wa Juna Sani A Katsina.

Daga Mohammad A. Isah.

Jaridar yanar gizo ta Katsina Times hadin gwiwa da cibiyoyin "Katsina Vocational Training Centre" da "Sardauna Katsina Foundation" sun shirya wa masu ta'ammuli da Kafofin sada zumunta na zamani a jihar taron kara wa juna sani.

Taron mai tagwayen taken "Yadda Mutum Zai Bunkasa Shafukansa na Yanar Gizo" da kuma "Aikin Dan Jarida" wanda ya gudana a dakin taro na Katsina Vocational Centre a ranar Asabar din nan 11 ga Nuwamba, 2023 ya samu halartar dimbin mahalarta da manyan bakin da suka gudanar da Lakcoci na ciki da wajen jihar.

Maudu'an da aka gabatar da Lakca a kansu a taron sun hada da: Gudummuwar kafafen sada zumunta ga inganta tsaro a jihar Katsina, Aikin Jarida da shafukan sada zumunta, Bincike ko hada rahoto na musamman da yadda ake yinsa, da kuma Muhimmancin amfani da ingantacciyar Hausa ko Turanci wajen rubuta Labari ko Sharhi.

Sauran maudu'an sun hada da: yadda ake yin bincike da samo labari, Tsaffi da Sabbin kafafen Labarai, Yadda mutum zai yi amfani da kafafen sada zumunta ya amfanar da kansa.

Wadanda suka gabatar da Lakcoci a taron kuwa sun hada da: Kakakin rundunar 'yansanda na shiyyar Arewa maso Yamma CSP Gambo Isah, Kwamishinan yada labarai na jiha Dakta Bala Salisu Zango, da kuma Editan jarida wanda ya fi dadewa a aiki editanci a Nijeriya Ibrahim Musa.

Sauran kuwa sun hada da: Malam Aliyu Saleh, Muhammadu Musa da sauransu.

Sama da Jaridun yanar gizo da masu wallafa labarai a shafukan sada zumunta 40 ne suka halarci taron, taron da aka shafe yini guda cur ana gudanarwa.

A yayin taron, an haska wasu maudu'an da aka gabatar da lacka a kansu ta hanyar Magiji, an kuma yi tambayoyi da jarabawa, tare da yin hotunan tarihi da bada shaidar halartar taron ga kafafen da suka halarta (wanda kamar yadda aka sanar zai riski kowanensu daga baya)

Post a Comment

0 Comments