Daga Wakilinmu Tare Da Katsina Daily News.
Ma'aikatar jin kai da kawar da talauci a Nijeriya, ta bayyana nasarar kammala wani binciken kuÉ—aÉ—en Ma'aikatan N-power bayan da ta sanya wasu kwararru kan harkar binciken Kudi suka tattaro mata bayanai da gane da kuÉ—aÉ—en albashin Ma'aikatan da ake zargin wasu sun danne.
Mr. Akindele ne ya bayyana hakan a lokacin da yi zama na musamman da wasu daga cikin Ma'aikatan N-power kamar yadda ministar jin kai Dr. Betta Edu ta tabbar wa Katsina Daily News, ZAMANI MEDIA ta ruwaito.
Ya ce "Labari mai daÉ—i da nake son bayyana maku a nan shi ne; kuÉ—aÉ—en (da aka sa a bincika) an kammala binciko su a jiya, kuma za ku sami hakkokan da kuke bi ba tare da wani 6ata lokaci ba." In ki shi.
"Za a fara biyan ma'aikatan N-power 'yan rukunin 'C' wadanda ke bin bashin kusan watanni 8 ba da wani dogon lokaci ba." Ya yi ta tabbatar
Mr. Akindele ya kuma bayyana cewar ministar jin kai, Dr. Betta Edu na matuƙar fafutukar ganin duk wasu hakkokan da suka rataya kan hukumar ta N-power da sauran muhimman kuduroran shugaban Bola Tinubu na kyautata rayuwar al'umma an aiwatar da shi yadda ya dace ba tare da wani jinkiri ba.
Ya kuma bayyana cewar, ba tare da 6ata lokaci ba za a kaddamar da wani sabon shirin N-power da za a dauki sama da mutum miliyan 5 kafin mulkin Shugaban kasa Tinubu ya kare.
0 Comments