Daga Mohammad A. Isah
Shugaba kasar Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin bada tallafin kuɗi ga magidanta miliyan 15, wanda hakan na a cikin manufofinsa da aka yi wa laƙabi da 'kyakkyawan fata'.
Tinubu ya kaddamar da shirin ne a ranar Talata a bikin ranar kawo karshen talauci na duniya, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Shugaban ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume yayin kaddamar da shirin.
In dai ba a manta ba, a jawabi shugaban a bikin samun Æ´ancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 2023, ya sanar da cewar shirin bada tallafin kuÉ—in zai fi mayar da hankali kan taimakawa marasa galihu.
Shugaba Tinubu ya shirya bikin tunawa da ranar kawar da talauci ta duniyar ne ta hanyar kaddamar da Conditional Cash Transfer ga magidanta miliyan 15.
In dai ana bibiyar ZAMANI MEDIA, a 'yan kwanakin nan mun kawo rahoton cewar, gwamnatin tarayya ta bakin ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr. Betta Edu, ta yi alkawarin kaddamar da shirin mika wa gidaje miliyan 15 na Conditional Cash Transfer kudi a ranar 17 ga Oktoba 2023 inda kowane mai cin gajiyar tallafin zai samu tallafin kudi na 25,000 har na tsawon watanni uku 75k.
Ministar ta ce za a bai wa kowane magidantci naira 25,000 har na tsawon watanni uku, wanda ya kai naira 75,000 Karkashin shirin Cash Conditional transfer.
Ta kuma ce nan ba da jimawa ba, za a kaddamar da wani tsarin bada tallafi mai suna 'Iya Loja Funds' wanda zai samarwa masu ƙananan sana'o'i bashin naira 50,000.
"Magidantan da Iyalansu sun kai yawan Æ´an Najeriya miliyan 62", In ji ta
Ranar 17 ga watan Oktoba dai ita ce ranar da Majalisar Ɗinkin duniya ta ware a matsayin ranar yaƙi da talauci ta duniya, don haka gwamnatin shugaba Tinubu da ofishin minista Betta Edu suka za6i ranar domin ƙaddamar da wannan shiri na rabon kuɗaɗe ga talakawa da marasa galihu bugu da kari don kuma rage radadin halin da cire tallafin manfetur ya jefa Talakawa ciki a kasar.
Sauran bayanan yadda shirin zai kasance, zai rika zuwa ne kaitsaye ta ofishin ministar bayan kaddamar da shirin, kodayake har ma wakililan shirin (enumerators) a wasu sassan kasar dsun soma ka6ar bayanan mutane suna yi masu rajistar shirin.
Waɗanda suka halarci bikin kaddamar da shirin sun haɗa da: ministar ma'aikatar ba da agaji da rage talauci Dr Betta Edu, ministan kuɗi Wale Edun, wakilin bankin duniya na ƙasashe, Shubham Chaudhuri, shugaban ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Matthias Schmale, da sauran manyan baki.
0 Comments