Mutane 2 Sun Mutu A Tankar Man Dizal A Kano.

Daga Wakilinmu

Wasu mutum biyu, Philip Osando, 40 da Philip Emmanuel, 35 sun mutu a cikin wata Tankar man dizel a shatale-talen Baban Gwari, da ke kan titin zuwa Katsina.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Ya ce hukumar ta samu wani kiran gaggawa da misalin karfe 8:20 na safe daga wani sufeto Abubakar Surajo wanda ya kai rahoton faruwar lamarin.

Ya ce, “A lokacin da jami’anmu suka isa yankin da misalin 8:20 sun gano wasu mutane biyu, Philip Osando dan kimanin shekaru 40 da kuma Philip Emernual dan kimanin shekaru 35 da haihuwa, wadanda suke harkokin kasuwancinsu kan titin Katsina.

“An ce wadanda abin ya shafa an musu alkawarin ba su kyautar man dizel amma kuma sai sun shiga cikin tankin dizal din don kwashe datti da dagelon da ke kasan tankin, shi ne suka shiga don cika sharadin da aka gindaya musu kafin su kar6i man dizal din. Lokacin da direban babbar motar ya iso sai ya yi kokarin kiran daya daga cikinsu a waya sai bai ji an daga wayar ba." In ji shi

Ya kara da cewsd “can kuma da aka duba cikin Tankin sai aka same su a kwance cikin tankin dizal sun suma. Daga nan ne aka yi kokarin fito da su, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.” In ji Kakin

Abdullahi ya kara da cewa an mika gawarwakin mutanen biyu ga Sufeto Abubakar Surajo na ofishin ‘Yansanda na karamar Hukumar Dala, yayin da ake ci gaba da bincike don gano musabbabin rasuwarsu.

Post a Comment

0 Comments