Daga Mohammad A. Isah.
An gudanar da taron Faretin girmamawa ga fiyayyen halitta Annabi (S) na shekara-shekara birnin Katsina.
Taron Faretin wanda 'yan'uwa Musulumi almajiran Sheikh Ibraheem Alzazaky na Katsina suka shirya na zuwa ne karo na 12, taron da aka gudanar a Filin ATC da ke kofar Kwaya a ranar Asabar din nan.
A yayin Faretin, Yara daliban Makarantun 'yan'uwa Musulmin ne da suka fito daga Makarantunsu na Fudiyyoyi da Islamiyyoyi ke fitowa suna taka Fareti; kowace Makaranta da salon Faretinta.
A Faretin Kowace Makaranta na fitowa da kalar tsarinta, Salato da kuma kalar 'unform' dinta wadda babu wata makaranta mai irinsu, sai su yi 'display'; in sun kammala su wuce.
Faretin na da tsarin alkalai da suke duba wasu abubuwa da suka hada da: yin rajista, Shiga(kaya), tsari, salo, kula da lokaci da sauran wasu sharudda.
A yayin faretin na bana sama da Makarantu 20 ne suka shiga rukunin masu Faretin, a yayin da Makarantu shida daga cikinsu suka yi Zarra, inda goda Uku rukunin na 'A' da 'B' da aka kasa su, suka zo 1, 2 da 3.
Wakilin 'yan'uwa Musulmi na Katsina, Shaikh Yakubu Yahaya wanda ya samu wakilincin Malam Shehu Dalhatu Usman ne ya kar6i Faretin, a yayin da sauran al'umma da Manyan baki da aka suka zo suka kasance masu kallon Faretin.
Kungiyoyi da sauran al'ummar gari ne suka halarci taron Faretin. Daga cikin kungiyoyin da suka halarci taron har ma suka yi tsokaci kan Faretin sun hada da: Malamin darikar Kadiriyya, wakilin Vigilante Group, Wakilin kungiyar taimakon kai da kai, wakiliyar kungiyar ANNAHDA, wakilin kungiyar wayar da kan al'umma ta jiha wato NOWA, wakilin 'yan Scout, da Wakilan kiristoci na kungiyar ETCN da Wakilin Cocin Ecwa.
Sauran baki a taron sun hada da Wakilan Kabilar Igbo da Fulani da sauran mutane maza da mata.
0 Comments