Daga Mohammad A. Isah.
Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda a ranar Talatar nan, ya kaddamar da rundunar tsaro ta musamman mai suna 'Katsina Community Watch Corps' a turance, a wani mataki na dawo da tsaro wanda ta6ar6arewarsa ke ta kara ta'azzara a jihar.
A jawabin da ya gabatar a yayin kaddamar da jami'an, gwamna Radda ya bayyana cewar samar da jami'an na daya daga cikin alkawullan da daukarwa 'yan jihar da zarar sun za6e shi a matsayin gwamnan jihar a yayin da yake yawon yakin neman za6en shekarar 2023 da ta gabata a kananan hukumomi 34 na jihar.
Duk a cikin jawabin nasa, gwaman ya kuma sha alwashin dawowa tare da tabbatar da tsaro a jihar baki daya ko da kudin jihar za su kare a wajen tsaron, inda ya ce wannan kaddamawar ta rukunin farko ce tukunna.
Radda ya kuma ya ja hankalin sabbin jami'an wadanda suka kasance matasa, a kan su gudanar da aikin bisa kishi da kwarewa don dawo da martabar tsaro mai dorewa a jihar.
Jami'an da suka suka kasance rukunin farko su kimanin 1500, gwamnan ya hada da kaddamar masu da Motoci masu sulke da ake kira da 'Armored Personnel Carriers' a turance, da motoci kirar Hilux guda 70 da kuma babura 700 don yaki da ta’addanci a fadin jihar Katsina.
Taron kaddamarwar wanda ya samu halartar baki na ciki da na wajen jihar, an gudanar da shi a filin wasa na Muhammadu Dikko Stadium da ke cikin birnin.
Manyan bakin da suka halarci taron sun hada da gwamnonin Kaduna, Kano, Zamfara, Jigawa, Kebbi, da Sokoto.
Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, Daraktan leken asiri na kasa NIA Alhaji Ahmed Rufa'i, Wakilin sufeto janar na 'yansanda da sauransu duk suna daga cikin wadanda suka halarci taron.
Sauran sun hada da Sarakunan gargajiya na Katsina da Daura, tsaffin gwamnonin, 'yan Majalisun jiha da na tarayya da sauran jami'an gwamnati.
0 Comments