Daga Mohammad A. Isah.
An yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta rungumi tare da karfafa harkokin fasaha da a halin yanzu duniya ke sauyawa zuwa gare su nan-da-nan.
Kamfanin Fasa, Kwarewa da zamanantar da rayuwar al'umma wato 'Vehance Technology Limited' da ke jihar Katsina, ta bakin shugaban Kamfanin, Kabir Muhammad Alhasan ne ya yi wannan kiran a wata fira da ZAMANI MEDIA ya yi da shi kan ayyukan Fasaha da Kamfanin ke yi a ranar Alhamis.
Kabir Muhammad ya ce, a yanzu kusan komi na duniya na canjawa ne zuwa fasaha mai tafiya da zamani, fasahar da ke canja Rayuwa, aiki, zamantakewa da kuma sana'a ko Kasuwancin al'umma.
Ya kara da cewa, saboda haka duk wani abu na ci gaba kamar irin wannan fasaha mai zamanatar da al'umma wadda ke ta kara bayyana a kullum a duniya, ya kamata gwamnati ta karfafe su ta kuma shige gaba wajen bada gudummuwarta don al'ummarta ta ci moriyarsu.
"Irin wadannan abubuwa (na Fasahar zamani) duk sadda suka taso, to sai fa gwamnati ta shiga sosai; ta ba da gudummuwa, ta karfafe su (sannan al'ummarta ta ci moriyarsu)."
'Vehance Technology' dai Kamfani ne na aiwatar da fasahar zamani gami da zamanantar da al'umma, wadanda suke yin dukkan aikace-aikacen fasaha da suka shafi tallata Hajoji a shafukan sada zumunta, hada manhajar siyar da Katin waya ko Data na yanar gizo, hada daudaukun Tsaro(CCTV), hadawa ababen hawa tsaro mai amfani da shacin yatsu ko kwayar ido ko motsi, Koyar da Ilimin Fasahar ita kanta, da kuma koyar da Kwamfuta zahirinta da badininta da sauransu.
"Burinmu shi ne zamantar da rayuwa da ayyukan yi ga al'ummar jihar Katsina." In ji shi.
0 Comments