Da Dumi-dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Jingine Shirin N-Power Baki Daya.


Gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da shirin N-Power baki daya, sai mama-ta-gani.

Betta Edu, ministar harkokin jin kai da yaki da fatara ce ta bayyana hakan a yayin da take jawabi a wani shirin a gidan Talabijin na TVC a ranar Asabar din nan.

Edu ta ce an dauki matakin ne sakamakon wasu kura-kurai a cikin shirin, inda ta ce gwamnati ta kaddamar da bincike kan yadda aka yi amfani da kudaden tun bayan fara shirin.

Ministan ta yi ikirarin cewa ba a samun wasu daga cikin wadanda suke cin gajiyar tallafin a wuraren ayyukansu, amma suna tsammanin biyan alawus na wata-wata.

Ta ce, “Dole ne mu koma mu duba N-Power mu fahimci mene ne matsalolin." In ji ta.

Ta ci gaba da cewa " don haka za mu dakatar da shirin a yanzu har sai an kammala binciken da ya dace kan yadda ake amfani da kudade a cikin shirin na N-Power." Ta sanar

“Muna so mu san mutane nawa ne a cikin shirin a yanzu, mutum nawa suke bin bashi da kuma adadin da suke bi. Muna sake fasalin N-Power gaba daya tare da fadada shi." Ta bayyanar.

“Akwai abubuwa da yawa da ke faruwa. Mun samu mutanen da ya kamata su bar shirin tun bara amma kuma har yanzu suna ci gaba da ikirarin cewa har yanzu suna koyarwa."

Da take bayyana takaicinta kan wadanda ba su zuwa aiki, Betta ta ce “Wani lokaci muna tuntuÉ“ar makarantar ko wuraren da suke aiki kuma ba sa nan. Ba sa aiki, amma har yanzu suna ci gaba da ikirarin cewa suna bin alawus-alawus na watanni takwas ko tara." In ji ta

“Kusan kashi 80% nasu ba sa aiki tukunna, amma suna neman albashi”. Ta cika da mamaki.

Post a Comment

0 Comments