Rundunar 'Yansandan Jihar Kano Ta Haramta Aiwatar Da Wasu Shagulgula A Jihar.

Daga Wakilinmu.

Rundunar 'yansanda jihar Kano, ta haramta aiwatar da da wasu shagulgula a fadin jihar baki daya.

ZAMANI MEDIA ta ruwaito cewar, shagulgulan da rundunar ta haramta a aiwatar da su a jihar sun hada da: Hawan Kilisa, Taka-ango da kuma Majalisi kowane iri har sai an nemi izinin hukumar kafin aiwatarwa.

Kwamishinan 'Yansandan jihar, CP Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifen bidiyo wanda jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya dora a shafinsa sada zumunta na Fesbuk.

"Muna ganin al'amurran ta6ar6arewar tsaro yana so ya dawo a cikin kwaryar Kano." In ji shi

"Mun lura da cewar Matasa suna karya Doka kuma suna amfani da wasu damarmaki su aikata wasu laifuffuka." Ya bayyanar.

Ya ci gaba da cewar, "Bincike ya nuna wa rundunar 'Yansanda cewar Hawan Kilisa, Hawan Angonci da zama na Majalisi, su ne wuraden da ake samun rashin jituwa (fadace-fadace) na matasa kuma ake aikata wadannan laifuffuka."

"Don haka a yau 7 ga Satumba, mun yi zama da majalissar Sarki cewar daga yau duk wanda zai hau Doki domin wadannan ababe, akwai ka'dodi da aka tanatar masu; sai sun tabbatar da su, an ba su izini kafin su je su aikata su saboda gudun 6atagari su shigo cikinsu su aikata aiki na cutar da al'umma."

Kwamishin ya kuma yi gardi da cewar, "duk wanda muka kama ya fito ya karya wannan Doka ba tare da ya je an tantance shi ba, to za a kama shi a gurfanar da shi a gaban Kuliya." 

Haka zalika kwamishinan ya kuma yaba tare da yi wa al'ummar jihar Kano godiya bisa ga hadin kai da suke ba wa rundunar don tsabtace jihar daga 6atagari wanda hakan baraza ne ga zaman lafiya da dukiyar al'ummar jihar.

Post a Comment

0 Comments