Maciji na ɗaya daga cikin halittun da Allah ya yi masu wata ke 6antacciyar baiwa ta musamman, a bangarori daban-daban. Misali:
Bincike ya tabbatar da cewar, Maciji yana iya ji da sauraren girgizar ƙasa daga ƙarƙashin ƙasa tsawon nisan mil 75, fiye da tsawon kwanaki biyar kenan kafin a yi girgizar ƙasa a inda za a yi ta.
Duk da Maciji ba shi da kunnen waje wato 'external ear' a turance na sauraren ƙara, amma bincike ya nuna alaƙa da kusancinsa da ƙasa ne da wani 'internal ear' ɗin sa ne suke ba shi wannan damar na jin wannan rugugin na girgizar ƙasar tsawon wannan nisan na mil 75.
Da yawan dabbobi masu kusanci da ƙasa irin su Ɓeraye da Zomaye, suna iya jin irin wannan motsin na girgizar ƙasa amma tsawon irin wannan kwanakin sai Maciji ne kaɗai yake iya jin hakan.
Har yanzu dai ba wani bincike a duniyar Kimiyya da Fasaha da aka samar da zai iya hasaso girgizar ƙasa kafin afkuwarta har ya kawowa yau ɗin nan, amma wannan halitta ta Maijici Allah ya hore masa hakan.
Ana dai gane akwai annobar girgizar ƙasa ta kusanto ne idan aka ga Maciji yana gudun ceton rai ba tare da an biyo shi ba, yana ƙaurace wa gidansa, yana cin karo da duk abin da yake gaban sa don dai ya samu ya tsira.
Bugu da kari, a ɓangare ɗaya, Macije ne dabba ta biyu a duniya da ta fi kashe ɗan Adam, a ɓangare ɗaya kuma ita ce dabba ɗaya tilo da Allah ya sa za ta iya hasaso annobar da tafi kashe ɗan Adam a duniya din.
Tsarki ya tabbata ga Allah maƙurar Hikima da buwaya!
0 Comments