Daga Wakilinmu.
Cristiano Ronaldo Ya samu kyakkyawar tarba a kasar jamhuriyyar Musulunci ta Iran a yayin da l'ummar Kasar suka yi dangon fari a masaukin 'yanwasan Al-Nassr a lokacin da suka isa Kasar.
Bayan saukar Kungiyar Kwallon kafa ta Al-Nassr, shi ko Cristian Ronaldo mai son addinin Islama ya ci gaba da ziyarar manyan masoyansa da suke mafarkin haduwa da shi a kasar ta Iran.
Cristiano ya fara ziyarar masoyansa, inda a ziyarar farko ya kai wa wata kwararriyar mai Zane-zane mai suna Fatemeh Homomi wadda ta dade tana yin zanensa duk da lalurar shanyewar jiki da ke gare ta.
Ziyararsa ta biyo kuwa, Cristiano ya ziyarci wani yaro ne wanda ke mafarkin ganinsa, dukkansu sun gana kuma sun yi hotunan Tarihi.
Ana sa ran shararren dan wasan Kwallon na Duniya, Ronaldo zai ci gaba da ziyarar Masoyansa a kasar ta a yayin wasan Kpfin yankin Asiya da Kasar Ta Iran ta kar6i bakuncinsa a wannan kakar.
Al-Nassr ce dai ƙungiya ta farko daga Saudiyya da ta je Iran cikin shekaru Bakwai saboda lalacewar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu, kafin lalacewar alakar ta gyaru a bana.
A yammacin ranar Talatar nan ne Al-Nassr za ta kara da ƙungiyar Persepolis a gasar wasan Zakarun Asiya a Iran.
0 Comments