An Kama 'Yan Wasan Real Madrid Da Zargin Lalata A Boye.

Hukumomin kasar Sipaniya sun kama wasu  'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid guda uku bisa zargin 'yin lalata da karamar yarinya a 6oye.

Kamar yadda fagen wasanni ta wallafa Zamani Media Crew kuma ta ruwaito, mahaifiyar wata yarinya mai karancin shekaru ta kai rahoto ga hukuma cewar, wani dan wasan Real Madrid ya dauki hoton Yarinyarta a lokacin da yake yin lalata da ita kuma ya sake shi.

Kawo wa yanzu dai kamar yadda rahotanni suka bayyana an kama 'yan wasan Real Madrid uku. A cikin 'yan wasan da shuka shiga hannu kan zargin lalatar da yarinyar akwai 'yanwasan karamar kungiyar, sai dai kamar yadda rahotannin sirri suka bayyanar ana iya samun karin 'yanwasa ciki har da 'yanwasa daga kungiyar farko ta Real Madrid.

Post a Comment

0 Comments