Mataimakin Shugaban babban ƙwamitin Zagayen Mauludi na Jihar Katsina, Sheikh Haruna Bakin-gida ya sanar da ranakun zagayen Mauludin jihar Katsina na wannan shekara a wajen Hatamar Miftahul Maulid da aka saba yi duk shekara a Katsina.
Rahoton da ZAMANI MEDIA ta samu, an bayyana yadda za a aiwatar da zagayen kamar haka:
1. Zagayen farko na Æ´an Islamiyyu zai kasance ranar Lahadi, 8 ga Oktoban 2023.
2. Zagayen Gidan Sheriff Abba Abu zai kasance ranar Litinin 9 ga Oktoban 2023.
3. Za a gabatar da Mauludin Jiha a ƙaramar Batagarawa, ranar Asabar 14 ga Oktoban 2023.
4. Sai Babban zagaye na gari duka zai kasance ranar Lahadi 15 Oktoban 2023.
An shawaraci ma'abota aiwatar da shagulgulan bikin Maulidin da cewar, don Allah su kiyaye lokacin fita da kammala zagayen, inda duk Maulidin da za a gudanar na zagaye zai rika farawa daga ƙarfe Takwas 8Am na safe, zuwa ƙarfe Shidda 6Pm na yammaci
Allah ya kara wa Annabi Muhammadu ï·º fadila da karama. Amin.
0 Comments