Sojojin da ke mulkin Nijar na ci gaba da neman goyon bayan ƙasashe musamman waɗanda ba su nuna adawa da juyin mulkin da suka yi ba a yankin Afirka ta Yamma.

Sojojin da ke mulkin Nijar na ci gaba da neman goyon bayan ƙasashe musamman waɗanda ba su nuna adawa da juyin mulkin da suka yi ba a yankin Afirka ta Yamma. 
      

Chadi ce ƙasa ta farko da Mahaman Lamine Zeine ya ziyarta bayan sojoji sun naɗa shi a matsayin firaministan Nijar

Sojojin da ke mulkin Nijar na ci gaba da neman goyon bayan ƙasashe musamman waɗanda ba su nuna adawa da juyin mulkin da suka yi ba a yankin Afirka ta Yamma.

A ranar Talata firaministan Nijar da sojoji suka naɗa, Ali Mahaman Lamine Zeine, tare da wasu mambobin majalisar mulkin soja biyu suka ziyarci Chadi domin tattaunawa da shugaban kasar, Janar Mahamat Idriss Deby.

Zeine - wanda ya je a matsayin fuskar diflomasiyya ta gwamnatin soja - ya ce a yanzu ƙasarsa na ƙarƙashin gwamnatin mulkin soji, yana mai cewa a shirye suke da su buɗe ƙofar tattaunawa.

Kazalika, sojojin mulkin sun tura wata tawaga zuwa Guinea ranar Asabar da ta gabata, duka dai da zimmar neman goyon baya.

Kafin haka, sabon ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Mody, ya je Mali a ranar Juma'a cikin wata gajeriyar ziyara.

Ƙasashen Mali da Burkina Faso da Gueinea mambobin Ecowas ne - ƙungiyar da ke raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma - amma ta takadar da su sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen.

Haka nan dukkansu sun ci alwashin goya wa Nijar baya idan dakarun Ecowas ko na wata ƙasar waje suka kai wa sojojin hari.

A ƙarshen makon da ya gabata gwamnatin sojan Mali ta sanar cewa za ta aika wa Nijar nau'in kayan abinci na hatsi kamar dawa masara da gero saboda takunkumin Ecowas da ya hana sayar mata da kayayyaki.

Chadi ba ta cikin ƙungiyar Ecowas, sannan kuma ba ta nuna adawa ƙarara da juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi ba, amma ta bayyana a fili cewa ba za ta goyi bayan yin amfani da ƙarfi a kan maƙwabciyar tata ba.

Har yanzu Ecowas na ci gaba da yunƙurin difilomasiyya don sasanta rikicin siyasar, duk da barazanar amfani da ƙarfin soja don taka wa sojojin ƙarƙashin Janar Abdourahmane Tchiani birki.

A ranar Alhamis da Juma'a hafsoshin tsaron ƙungiyar za su yi taro a birnin Accra na Ghana don ci gaba da tattaunawa bayan shugabannin Ecowas ɗin sun ba su umarnin ɗaura ɗamarar kutsawa Nijar a makon da ya gabata.

A gefe guda kuma, fitattun mutane da ƙungiyoyi a Najeriya na ci gaba da nuna adawa da yin amfani da ƙarfin yayin da Shugaba Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban Ecowas, yake jagorantar yunƙurin.

Post a Comment

0 Comments