Shugaba Bazoum ya gana da likitansa

Shugaba Bazoum ya gana da likitansa
  

Magoya bayan hamɓararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum sun ce likitansa ya kai masa ziyara domin duba lafiyarsa.Kamfanin dillancin labaran Faransa ya kuma bayyana cewa likitan ya yi wa Mista Bazoum da matarsa da ɗansa guzirin abincin gargajiya da shugaban ya fi so a inda suke tsare.

Baya ga abinci da suka kunshi gayyaki da likitan ya kai wa hambararren shugaban na Nijar, ya kuma kai masa magungunna.

Likitan ya kuma nuna damuwa kan yanayin wurin da ake tsare da Bazoum a wani ɗakin ƙarƙashin ƙasa da ke fadar shubaban ƙasar a birnin Yamai inda ko lantarki babu.

Sojojin dai na tsare ne da Bazoum da iyalinsa da kuma dansa mai shekara 20, kuma tun bayan da suka ƙwaci mulki a hannunsa a ranar 26 ga watan Yuli suke tsare da shi.

Kasashen duniya, ciki har da Amurka, da Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da nuna damuwa game da lafiyar zaɓaɓɓen shugaban da kuma lafiyar iyalinsa.

Tuni dai hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce rahotannin da ake ruwaitowa kan yanayin da ake tsare da Bazoum sun saɓa wa dokokinta na kare hakkin dan adam.

Wasu rahotanni da BBC ba ta tabbatar ba, sun ce sojojin da suka hambarar da Bazoum suna tilasta masa cin busasshiyar shinkafa da taliya.

Masharhanta dai na ganin matsin lamba ga sojojin na Nijar ne ya sa suka ba Bazoum damar ganawa da likitan nasa.

Post a Comment

0 Comments