Daga Muhiddeen.
Wannan matar da kuke gani sunanta Jill Price, shekarunta 58 amma ba ta manta komai, duk abun da ya faru a rayuwarta yana cikin ƙwaƙwalwarta a ajiye kamar yanzu yake faruwa.
Idan ka tambaye ta me ya faru tun daga shekarar 1980 har zuwa yau, za ta karanto maka tsaf kamar a littafi ba tare da ta tsallake rana É—aya ko wani al'amari guda É—aya ba.
Za ta faɗa maka irin abincin da ta ci ko irin tufafin da ta saka shekaru 50 da suka gabata a irin wannan ranar. Ita kamar na'ura haka ƙwaƙwalwarta take, ba ta manta komai, komin ƙanƙantar abu ba ta mantawa. Kamar yadda ake recording video a camera, ka san ba zai tsallake komai ba ko? To ita ma haka take.
Likitoci sun tabbatar da cewa tana fama da wata larura mai suna hyperthymesia, wacce ke sa mutum ba zai taɓa manta abun da ya faru a rayuwarsa ba ko da ya so hakan.
Shafin Wikipedia ya ce zuwa 2021 mutane 62 ne kacal aka taɓa aunawa masu wannan larurar a duniya, kuma Jill Price ce mutum ta farko da aka fara aunawa tare da samunta da wannan larurar.
A shekarar 2008 Jill Price ta rubuta littafi sukutum game da rayuwarta tare da taimakon Bart Daris mai suna, The Woman Who Can't Forget.
0 Comments