Rahotanni daga jihar Katsina na bayyana cewar wata kwarya-kwaryar zanga-zanga ta 6arke a unguwar Sabuwar unguwa Katsina, da rana kata a ranar Larabar nan.
Al'ummar sabuwar unguwa da ke filin Kanada a cikin birnin Katsina ne suka fito ne zanga-zangar domin nuna fushinsu da kuma rashin amincewarsu kan ginin wani Masallacin Juma'a a da ake shirin yi a Filin da suka ce an tanada don gina Sakandare da kuma Ofishin 'yansanda (Out Post).
Hoto: Sama'ila Sector
0 Comments