'Yan bindiga sun hallaka 'yan sintiri 22 a jihar Zamfara
Wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai, sun afka wa mutanen kauyen Sakida na karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, inda suka farmaki manoma da suka je gonakinsu don shuka.
Wannan harin, shi ne mafi muni, tun bayan da aka rantsar da Dauda Lawal Dare a matsayin Gwamnan jihar Zamfara, da ya daukar alkawurran cewa tsaro, shi ne abu na farko da zai tunkara idan ya yi nasarar zabe.
Wani mazaunin yankin Ahmad Muhammad Jambako, ya shaida wa DCL Hausa ta wayar salula cewa dama 'yan bindigar sun sanar da hana mutanen yankin noma, inda suka ci su tarar kudi, wadda sai sun biya sannan su amince su yi noma a yankin.
Majiyar ta DCL Hausa ta ce a lokacin wannan hari a kauyen Sakida ne, mutanen kauyen suka nemi agaji daga 'yan sa kai na garin Jambako domin kawo musu daukin gaggawa.
Lokacin da 'yan sa kan ke hanyarsu ta zuwa garin Sakida, ashe 'yan bindigar sun yi kwanton bauna, inda suka harbe mutane kusan 22.
0 Comments